[...] "Ina da shawara." Ya sunkuyo gaba kamar yadda ƙawa ta Afrilu ke yi lokacin da take son bayyana sirri, duk da cewa babu wani sirrin ta da ke da ɗaɗi. ko ma sirrin gaske. "Idan ba ka gaya wa kowa ina nan ba, zan iya gyara idanun ka." "Fita daga gari!" Ya ƙifta sau da yawa. "Abin da nake ƙoƙarin yi kenan." "Abin da nake nufi shine ba za ka iya yin hakan ba!" "Me zai hana?" "To, babu wanda ya iya gyara idanu na, sai da tabarau." “Ina da wata baiwa. za ka gani, idan har…” "...Ban gaya wa kowa game da kai ba?" "Wannan shine tushen maganar, wannan haka yake." “Ta yaya zan san ba za ka makantar da ni ba? Ta yiwu kai ma kamar masu tallan waya ka ke masu yin alkawuran ƙarya. " Ya sake fara kumbura yana sacewa. "Ba zan yiwa halittar da ba ta cutar da ni haka ba." "Ma'ana idan na cutar da kai, za ka iya makanta ni?" "Ya danganta da buƙatar sanin hakan." "Kuma idan ka gyaran ido na, kuma ban gaya wa kowa game da kai ba, za ka bar filayen mu?" "Wannan ita ce magana!" [...] | Entry #38519 — Discuss 0 — Variant: Kanokanoo
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
4 | 1 x4 | 0 | 0 |
|
[...] "Ina da shawara." Ya yi gaba kamar yadda abokina Afrilu yake yi lokacin da take son faɗan sirri, duk da cewa babu wani sirrin da ke da kyau. Ko ma sirrin gaske. "Idan baki gaya wa kowa ina nan ba, zan iya gyara idanunku." "Fita daga gari!" Ya ƙifta ido sau biyu. "Abin da nake ƙoƙarin yi ke nan." "Abin da nake nufi shine ba za ku iya yin hakan ba!" "Me yasa?" "To, babu wanda ya iya gyara min idanuwana, sai dai tabaro." “Ina da wasu ƙwarewa. Za ku gani, matuƙar…” "...Kar na faɗa wa kowa game da ku?" "Wannan ita ce kan batun, wato nub." “Ta yaya zan san ba za ku makantar da ni ba? Kuna iya zama kamar ɗaya daga cikin waɗancan masu tallan telefon suna yin alƙawari amma gaba ɗaya ƙarya.” Ya fara kumbura, yana sake kashewa. "Ba zan yi irin wannan abu ga wata halitta da ba ta cutar da ni ba." "Ma'ana idan na cutar da ke, za ki iya makantar da ni?" "Wannan akan buƙatan-sani ne." "Kuma idan kun gyara idanuna, kuma ban faɗa wa kowa game da ku ba, za ku bar gonakinmu?" "Wannan shine kan batun!" [...] | Entry #38533 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
2 | 0 | 1 x2 | 0 |
|
[...] “Ina da shawara.” Ya jingina gaba kamar yadda abokiyata Afrilu ke yi lokacin da take son faɗan wani sirri, duk da cewar babu wani sirrinta da ke wani amfani. Ko a ce ma sirri ne da gaske. “Idan baka gaya wa kowa ina nan ba, zan iya gyara idanuwanka.” “Bar garin!” Ya lumshe sau da dama. "Abin da nake ƙoƙarin yi ke nan.” “Abin da nake nufi shine ba za ka iya yin hakan ba!" “Me ya hana?" "To, babu wanda ya taɓa iya gyara idanuwana, banda gilashin." “Ina da wasu baiwa. Za ka gani, muddin...” “…Ban gaya wa kowa game da kai ba?” “Wannan shine ainihin batun, shine zancen.” “Ta yaya zan san ba za ka maƙantar da ni ba? Kana iya zama kamar ɗaya daga cikin waɗancan masu tallan kan-layi suna yin alƙawura amma gabaɗaya ƙarya ne.” Maimaicin ya fara kuma. “Ba zan yi irin wannan abu ga wani halitta da bai cutar da ni ba." “Ma'ana idan na cutar da kai, za ka iya sa ni in maƙanta?” “Wannan akan buƙatar neman-sani ne.” “Kuma idan ka gyara idanuwana, kuma ban gaya wa kowa game da kai ba, za ka bar gonakinmu?” “Wannan shine ainihin batun!” [...] | Entry #38534 — Discuss 0 — Variant: Kanokanoo
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
1 | 0 | 0 | 1 x1 |
|
[...] “Ina da wata shawara.” Sai ta matso kusa tamkar dai yadda ƙawata Harira take matsawo idan tana so ta faɗa min wani sirri, duk da cewa ba wani daga ciki sirrikanta da yake mai kyau. Ko kuma ma ka kira shi da sirri. “Idan baki gaya wa kowa ba na zo ne domin in gyara miki idonki!” Ya ƙifta na wasu lokuta. “Wannan shi ne abinda nake ƙoƙarin yi.” “Abinda nake nufi shine ba za ki iya haka ba!” “Saboda me?” “To, babu ya taɓa iya gyara ido na in ba tabarauna ba.” “Ni gwana ce. Za ki gani, na nuna miki…” “…Babu wanda ya taɓa ba wa labarinki?” “Wannan shi ne muhimmin abu, wannan ne ginshiƙi.” “Ta yaya zan sani cewa ba za ki makantar da ni ba? Ki zama kamar ɗan magori, wasa-kanka-da-kanka ki yi alƙawari amma ki saɓa.” Sai ya ɓace ya dawo ya ɓace ya dawo. “Babu halittar da zan yi wa wannan musamman wanda bai cuce ni ba.” “Kina nufin idan na cuce ki, za ki makantar da ni?” “Ina buƙatar sannin wannan.” “Kuma idan kika gyara min idanuwa na, kuma ba wanda na yi wa bayninki, za ki bar inda wurinmu?” “Wannan shi ne jigon abin!” [...] | Entry #38230 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
0 | 0 | 0 | 0 |
|